Mahawara kan batar dabon dalla billiyan 20 a Najeriya
February 5, 2014A yanayin da ke nuna kara fuskantar rashin tabbas a kan zahirin kudadden man fetir din da a ke zargin sun salwanta, gwamnan babban bankin Najeriya ya sake dagewa kan cewa dalla bilyan 20 ne suka bata kuma basu kaiga shiga asusun gwamnatin Najeriyar ba.
Kwan gaba kwan bayan da ake ci gaba da fuskanta a kan batar dabon da wadannan makuddan kudadde suka yi da ya sanya nunawa juna 'yar yatsa a tsakanin gwamnan babban bankin Najeriya Sunusi Lamido Sunusi da kamfanin kula da albarkatun mai na Najeriyar NNPC.
Tuni dai kungiyoyin da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriyar suka bayyana damuwarsu a kan abin da suka kira kara zurmewa da kasar ke yi a fanin yaki da cin hanci da rashawa. Malam Awwal Musa Rafsanjani na gamayyar kungiyoyin yaki da cin hanci da Zero Coalition ya yi karin bayani kamar haka.
"Wannan na nuna mana cewa cin hanci da rashawa a Najeriya ya riga ya kankama kuma ba tsoron Allah a cikin wannan al'ammari , mu muna ganin wannan cin amana ce ta 'yan Najeriya, kuma ba yadda za'a yi a samu ci gaba da wannan barna da wannan sata da ake yi. Dole ne sai an dau mataki a matsayinmu na kungiyar da ke yaki da cin hanci da rashawa zamu ci gaba da fafutukar cewa dole ne gwamnati ta tashi ta yi wani abu a kai''.
Kamfanin NNPC ya ce akwai rashin fahimta
Tuni dai kamfanin na NNPC ya sake jan daga yana mai cewa akwai fa rashin fahimta a kan kudadden da ake Magana domin ba wai bata suka yi ko an sace su ba, kamar yadda Mr Andrew Yakubu manajan daraktan kamafanin na NNPC ya bayyana.
"Yace ai mun bayyana cewa wannan adadin kudi ne da suke a kamfanin LPDC na gas na Najeriya ba wani sabon abu bane, akwai bukatar fahimtar bambancin da ke tsakanin haka, kuma ma ai akawai haraji da ke zuwa ga gwamnati kamar yadda a ke a kowane sashi''.
To sai dai gwamman babban banki yace sun fa samar da cikakken shaida a kan wannan adadai na kudi kuma Magana daya suke yi cewa dalla bilyan 20 ne suka bata.
"Mun samar da shaida a kan duk wannan batu na adadin maid a kamfanain NNPC ya fitar day a kai dalla bilyan 60, amma dalla bilyan arabain aka sanya a asusun gwamnati, maganar da muke it ace ina aka kai sauran dalla bilyan 20 da suka yi batar dabo"
Wannan tonon silili da ya gwamnan babban bankin Najeriyar ya yi da ya sanya bankado zargin masu halin bera da suka afka kan dukiyar man ta Najeriya, abin da ya harzuka fadar gwamnatin Najeriyar ta Aso Rock har ma da yiwa Sanusin barazana, to sai dai ga Hon Aliyu Gebi ya ce kamata ya yi a yaba da wannan lamari.
"Batun zargin karkatar da kudadden man fetir din Najeriyar dai na kara bayyana zahirin yadda ake wa kaci wa tashi da dukiyar Najeriyar, da a kullum talakan kasar ke kara shiga hali na rashin tabbas saboda matsalar cin hanci da rsahawa".
A yayinda ake sa ido don ganin matakin da gwamnati zata dauka a kan wannan batu, tuni an fara ganin tasirinsa a majalisar wakilan Najeriya da ta dage lallai sai an sanya kasafin kudin ma'aikatun biyu da ake takadamma a kansu kafin su fara muhawa a kan kasafin kudin.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Pinaɗo Abdu Waba