1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Mace-mace na karuwa a Rafah saboda luguden wuta na Isra'ila

Mahmud Yaya Azare MAB
February 9, 2024

Jiragen yakin Isra'ila sun karkata farmakinsu zuwa yankin Rafah da ke kan iyakar Masar da Gaza biyo bayan watsewa baram-baram a yunkurin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar firsinoni tsakanin Isra'ila da Gaza.

https://p.dw.com/p/4cEUU
Falasdinawa na nuna jimamin mutuwar 'yan uwansu a Rafah
Falasdinawa na nuna jimamin mutuwar 'yan uwansu a RafahHoto: Mohammed Talatene/dpa/picture alliance

Ministocin kasashen Masar da Amurka da Qatar da Isra'ila sun yi a zama a birnin Alkahiran Masar kan yunkurin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Gaza, amma an watse ba tare da cimma biyan bukata ba. Saboda haka ne jiragen yakin Isra'ila suka karkata akalar farmakinsu zuwa yankin Rafah da ke kan iyakar Masar daGaza, duk da gargadin da kasashen

Karin bayaniGaza: Kokarin tsagaita wuta mai dogon zango

Jiragen yakin Isra'ila sun ta yin luguden wuta tun da daren Alhamis zuwa Jumma'a a Rafah da ke zama tudun na tsira daya tilo da ya rage wa dubu dubatan Falalsdinawan Gaza. Dama samamen dakarun Isra'ila da luguden wutar sun kwashe watanni hudu suna yi a kansu ya tilasta musu fakewa da yanki na Rafah.

Karin bayani: Gaza: Za a cimma wata yarjejeniyar tsagaita wuta

Isra'ilana zargin cewa jagororin Hamas da take nema ruwa a jallo sun sulale daga yankin Khan Yunus na tsakiyar Zirin Gaza da yanzu take mamaye da shi.