Ma'aikatan Lufthansa sun kira yajin aiki
November 14, 2016Kungiyar ma'aikata da masu tuka jiragen sama na kamfanin Lufthansa sun shiga yajin aiki abin da baya rasa nasaba da neman karin albashi da ake ta cece-kuce a kansa tsawon lokaci. Kungiyar ma'aikatan dai ta bayyana cewa nan da ba dadewa ba ne cikin sa'oi 24 za su bayyana tsawon lokaci da yajin aikin nasu zai dauka.
Ita dai kungiyar matukan jiragen na neman kari na kashi 3.66 cikin dari na albashinsu a shekara. Abin da ake ta fama a kansa sama da shekaru biyar. A cewar kungiyar direbobin kamfanin na Lufthansa na ta kara kirga riba yayin da ma'aikata ke fama da karin kudi wajen siyen kayan bukata.
A shafin kungiyar na Twitter ta bayyana cewa wannan shi ne karo na 14 tun da take kira na zuwa yajin aiki daga watan Afrilu na shekarar 2014. Bayan mako guda na yajin aiki na kamfanin a watan Nuwamba 2015, an soke jirage 4,600 abin da ya shafi fasinjoji rabin miliyan.