Musanyen wutsa tsakanin bangarori masu rikici a Libiya
April 17, 2019An fara jin karar makamai cikin unguwanni masu dauke da dandazan mutane a birnin Tripoli na kasar Libiya, bayan kwashe makonni biyu ana artabu tsakanin dakarun gwamnatin da ke samun tallafin Majalisar Dinkin Duniya gami da na Janar Khalifa Haftar wanda yake rike da wasu sassan na kasar ta Libiya mai fama da tashe-tashen hankula.
Kusan mutane 190 suka halaka cikin makonnin biyu da aka kwashe ana musanyen wutsa tsakanin bangarorin da ke rikici a cewa wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, yayin da wasu fiye da 800 suka jikata. Jami'an diplomasiyya sun ce yaduwar rikicin na kara kassara duk wani shirin neman samar da zaman lafiya.
Kasar ta Libiya da ke yankin arewa Afirka ta fada cikin rudani tun shekara ta 2011 bayan kawo karshen gwamnatin Marigayi Shugaba Muammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40.