1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Littafi kan Mandela ya janyo rikici

July 23, 2017

Wasu dangin marigayin shugaba Nelson Mandela, sun soki littafin da wani likita ya rubuta kan halin jinyar marigayin tun kafin mutuwarsa, suna mai cewa hakan ya ci karo da amanar da ke tsakanin mara lafiya da kuma likita.

https://p.dw.com/p/2h1aH
Bildergalerie Nelson Mandela 93 Geburtstag
Hoto: picture-alliance/dpa

Wasu daga cikin dangin marigayin shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela, sun soki littafin da wani likitan soja ya rubuta kan halin jinyar marigayin tun kafin mutuwarsa, suna mai cewa hakan ya ci karo da amanar da ke tsakanin mara lafiya da kuma likita. Marubucin littafin ya bayyana irin takaddamar da aka yi ta samu tsakanin bangaren na Mandela da likitoci, musamman gabanin mutuwar marigayin.

Likitan mai murabus Vejay Ramlakan, ya kuma ce ya rubuta littafin ne bayan bukatar yin hakan da wasu daga iyalan na Nelson Mandela suka yi. Wani jikan jagoran sauyin na Afirka ta Kudu Nkosi Mandela, ya ce a fahimtarsa da littafin ya saba ka'idar aikin likita. Ita ma a nata bangaren, uwar gidan marigayi Nelson Mandela, Graca Machel, ta ce tana nazarin kai maganar gaban kuliya.