Libya: Mutane 121 sun rasu a rikicin Tripoli
April 14, 2019Talla
Kamfanin dillancin Labaran Faransa na AFP ya rawaito cewa yanzu haka ana can ana ci gaba da gwabza fada a wasu unguwannin kudancin birnin na Tripoli inda kowane bangare ke ikararin samun nasara a fagen daga, sai dai kuma alamu na nuni da cewa babu wata gagarumar nasara da wani bangare ya samu kan abokin gabarsa.
Hukumar Lafiya ta Duniya reshen kasar ta Libiya dai ta yi tir da kuma yin Allah wadai da yawan buda wutar da masu fadan ke yi a kasar wanda ta ce ya na shafar motocin kiwon lafiya da ke kai-komo wajen agazawa wanda suka jikkata.