1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'umma cikin matsin rayuwa a Libiya

Mahmud Yaya Azare LMJ
August 26, 2020

Daruruwan mutane a birnin Tripoli na Libiya, sun gudanar da zanga-zangar neman gwamnatin hadin kan kasar da ke karkashin Fayez al-Sarraj da ta dauki matakan rage musu wahalar rayuwa.

https://p.dw.com/p/3hYCc
Libyen Protest gegen Gaddafi 2011
Zanga-zangar adawa da gwamnatin hadaka a LibiyaHoto: picture-alliance/dpa/M. Messara

Masu zanga-zangar neman saukin matsin rayuwar a Libiyan dai, sun yi dandazo a dandalin shuhada da ke tsakiyar birnin Tripoli na kasar ta Libiya, inda suke kokawa da yanayin matsanancin halin rayuwa da suka tsinci kansu cikinsa sakamakon abun da suka kira gazawar gwamnatin hadaka a karkashin ikon Fayez al-Sarraj. Suna dai zargin gwamnatin da cuwa-cuwa da kuma fifita bukatun  sojojin haya na ketare a kan bukatun talakawa.

Talaka ba ya samun wuta da ruwa

Kusan watanni uku ke nan dai, tun bayan da madugun 'yan tawayen kasar, Janar Khalifa Haftar ya katsewa birnin na Tripoli ruwan sha da iskar gas din da ke samar da wutar lantarki, hakan ta sanya mazauna birnin da suka kai miliyan biyu ke zaune cikin halin duhu dudum, sai dai masu galihu da ke kunna injinan janareto, kamar yadda wurare da dama suka daina samun ruwan sha mai tsafta sai na rijiya.

MDD ta caccaki kasashen da ke da hannu a rikicin Libiya

An dai raunata wasu daga cikin masu zanga-zangar da aka kwashe tsawon kwanaki hudu a jere ana yinta. Wannan zanga-zanga dai na gudan ne ba a birnin na Tripoli kadai ba, har ma da biranen Sabaratah da Zawiya da ke yammacin kasar.

Libyen Minsterpräsident Fayiz as-Sarradsch
Jagoran gwamnatin hadin kan kasar Libiya Fayez al-SarrajHoto: AFP

Shugaban gwamnatin hadin kan kasar Fayez al-Sarraj wanda ya sanar da yin garambawul a majalisar ministocinsa, ya zargi wasu da ya ce makiyan kasar ne da kokarin tayar da fitina, adaidadai lokacin da kasar ke cikin halin yakin da yace an tilastawa musu yin sa: "Muna sake maimaita cewa, bukatun da mutane ke zanga-zanga a kansu na neman kayayyakin more rayuwa abu ne da ke kan doka. Muna kuma iya kokarinmu domin magance su.

Libiya: Kawo karshen yakin basasa

Amma ya kamata mu yi la'akari da cewa, madugun 'yan tawaye Haftar wanda ya yi fatali da tayin tsagaita wutar da mukai ta yi masa, shi ne ummul haba'isin katsewa mutane wuta da ruwa, kamar yadda yake ci gaba da hakar mai wanda shi ne hanya daya tilo ta samarwa 'yan Libiya abinci."

Kashewa sojojin kasashen waje kudi?

To sai dai masu adawa na kalubalantar gwamnatin hadin kan kasar da fifita bukatun sojojin hayar da Turkiya ke kawo mata da daukar nauyin kafa sansanonin Turkiya a kasar, abubuwan da suka ce sune suka jawo wannan mawuyacin halin da' yan Libiyan ke ciki: "Abun takaici cin-hanci da rashawa ya mamaye ko ina a wanan gwamnati. Lamarin da har yakai ga gwamnatin na sanarwa 'yan kasa cewa, ta bai wa sojojin hayar dalar Amirka miliyan 40, adaidai lokacin da mutane ke layin neman karbar kudainsu a bankunan da suka karye."