Libiya: Taron majalisar ministoci cikin rudani
April 21, 2022Talla
Shugaba Fathi Bachagha da kansa ne ya jagoranci taron, wanda ya kira a sahihance bayan da suka samu tabarrukin majlisar dokokin gabashin kasar, mai tazarar kilo mita 750 da birnin Tripoli.
Ita dai Libiya ta fada rudanin jagoranci ne tun bayan da hamshakin attajiri Abdelhamid Dbeibah da ke jan ragamar mulki a birnin Tripoli tun a shekarar 2020 ya yi kwance da mukaminsa, bayan da majalisar dokoki mai mazauni a birnin Sebha ta nada Bachagha a matsayin sabon firaminista.
Duk da cewa ba shi da wani karfin fada a ji da bangaren zartarwa a birnin Tripoli, firaminista Fathi Bachagha ya ce zai ci gaba da tafiyar da harkokin mulki kamar yadda majalisar ta bukata.