Mayar da bakin haure gida daga Libiya
July 30, 2024A wani yunkurin magance matsalar bakin haure kasar Libiya ta mayar da bakin haure 369 zuwa kasashen Najeriya da Mali wadanda suka hada da mata fiye da 100 gami da yara. Wani jami'in kasar Mohammed Baredaa a ma'aikatar harkokin cikin gida na Libiya, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa jiragen saman sun kwashe mutane 204 zuwa Najeriya sannan wasu 165 zuwa kasar Mali.
Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kauran jama'a ta samar da jiragen saman da suka bayar da bakin haure zuwa kasashensu na Najeriya da Mali, a cikin wani shiri na mayar da bakin gida bisa radin kansu, maimakon kasadar tsallaka teku domin shiga kasashen Turai, abin da ke janyo cin zarafin bakin haure daga masu fataucin mutane da kwace musu dukiya gami da tilasta musu aikin bauta, kana wasu lokuta bakin haure kan rasa rayukansu a wannan tafiya mai cike da hadari na neman zuwa kasashen Turai.