1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: Korar wasu kamfanonin Turai

Ramatu Garba Baba
May 13, 2019

Mako guda bayan da ya dawo daga rangadi a kasashen Turai, Shugaban Hukumar Hadin kan kasa na Libiya Fa'eez Sarraj, ya haramtawa wasu kamfanonin kasashen Turai sama da 40 gudanar da harkokinsu a kasar.

https://p.dw.com/p/3IOWK
Libyen zerstörtes Gebäude in Tripoli
Rikici ya jima da wargaza kasar ta LibiyaHoto: Imago

Shugaban Hukumar Hadin kan kasar ta Libiya, Fa'eez Sarraj ne ya bayar da wannan umarnin. Cikin kamfanonin da aka takatar din har da kamfanin mai na Total mallakin Faransa. Mafi yawan kamfanonin da aka haramtawa aiki a kasar ta Libiya dai, na kasashen Faransa da Jamus da kuma Finland ne.

Wata majiya na cewa hakan alama ce da ke tabbatar da cewa firaministan bai gamsu da sakamakon ganawarsa da shugabannin wadannan kasashen ba. Sanarwar ta kara da cewa, wadannan kamfanonin sun ci gaba da gudanar da harkokinsu a Libiya, duk da cewa yarjejeniyoyin da ke tsakaninsu da kasar sun daina aiki tun a shekara ta 2010.

A yanzu dai an bai wa wadannan kamfanoni da suka hadar da Total na Faransa da Siemens na Jamus da kuma Alcatel wanda reshen kamfanin Nokia na kasar Finland ne, wa’adin watanni uku domin sabunta lasisi matukar suna bukatar gudanar da ayyukansu a kasar ta Libiya.