Kwale-kwale ya kife da bakin haure a Libiya
July 25, 2019Talla
Jami'an da ke tsaron gabar ruwa a Libiya sun tabbatar da mutuwar mutum daya yayin da aka ceto mutane 134 da suka fada ruwa, yawancin wadan da aka ceto 'yan kasashen Afirka ne da Larabawa. Kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya IOM ta kiyasata bakin haure 426 sun mutu a tsakiyar tekun bahrum a shekarar 2019 ka dai a yunkurin shiga nahiyar Turai.