Libiya: Shekara 11 da kadawar guguwar juyin-juya hali
February 17, 2022Talla
Al'ummar kasar Libya sun gudanar da taron cike da alhini kan halin da kasar ta tsinci kanta na rikici da kuma rashin tabbas. A rana mai kamar haka 17.02.2011 guguwar juyin juya halin da tayi sanadiyar kifar da gwamnatin Moammar Ghadhafi.
A waiwaye adon tafiya, jama'ar kasar da dama sun amince, ba a sami ingantaciyyar demokradiyya kamar yadda aka yi zato ba, maimakon hakan, Libiya ta fada cikin rikicin da har yanzu ba a iya shawo kansa ba.
Bikin tuni da ranar a bana, ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fama da rikici na jayyaya kan shugabanci a tsakanin bangarori biyu da kuma barakar da aka samu a baya-bayan nan kan nadin sabon firaiminista bayan soke zaben da aka shirya gudanarwa a kasar a watan Disambar bara.