Yakin na kara kassara Libiya
January 26, 2020Talla
Ma'aikatar man kasar ta Libiya ta yi kisayasin asrar sama da dala miliyan 255 cikin kwanaki shida bayan rufe aikin rijiyoyin man kasar. Rufe aikin rijiyoyin man ya zo ne bayan da dakarun babban dan tawaye Khalifa Haftar suka karbe iko da tashoshin fidda mai da ke gabashin kasar. A cewar kamfanin man fetur din Libiya, bayan rufe rijiyoyin man sun kiyasta a ko wace rana an yi asara ta dalar Amirka sama da miliyan 42. Sai dai a ranar Alhamis din nan an kawo karshen datse tashoshin fidda man wanda Khalifa Haftar ya yi.