Kasashen duniya na maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta
October 23, 2020Majalisar Dinkin Duniya ta ce yau rana ce mai matukar mahinmanci ga duniya a bisa nasarar da aka cimma na tsagaita bude wuta, a yayin da Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da matsayar da bangarorin da ke jayayya da juna suka cimma na rattaba hannu kan yarjejeniyar. Kungiyar ta ce tana fatan ganin, nan bada jimawa ba, za su hau teburin sulhu don ci gaba da tattauna batun zaman lafiya.Kasar Turkiyya kuwa ta baiyana rashin ingancin yarjejeniyar.
Kwanaki biyar dai aka kwashe ana tattaunawa a tsakanin bangarorin da ake jayayyar mulki a birnin Geneva na kasar Switzerland bisa jagorancin wakilan Majalisar Dinkin Duniya. Libya dai ta tsunduma cikin rikici ne, tun bayan hambarra da kisan Shugaban kasar Moamer Ghadafi a shekarar 2011 tun daga wancan lokacin aka samu bullar sojojin sa kai da suka raba kasar gida biyu. Ana dai kallon kokarin kawo karshen rikicin Libyan a wani misali na kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Kungiyar tarayyar Turai da kungiyar hadin kan Afirka.