Farfado da dangantakar Jamus da Libiya
September 9, 2021Talla
Ministan harkokin kasashen ketare na Jamus din Heiko Maas ne ya sake bude ofishin jakadancin a Tripoli babban birnin kasar ta Libiya. A cewar Maas Jamus ta dauki wannan matakin ne, ganin irin ci-gaba mai ma'ana da aka samu a Libiyan a shekarar da ta gabata. Libiyan dai ta tsinci kanta cikin yakin basasa, bayan kifar da gawamnatin tsohon shugaban kasar marigayi Muammar al-Gaddafi a shekara ta 2011. Koda yake an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Libiyan a shekarar da ta gabata ta 2020, tare da kafa gwamnatin rikon kwarya da za ta jagoranci zaben da za a gudanar a kasar a ranar 24 ga watan Disambar wannan shekarar da muke ciki.