Bukatar Libiya ta yi da sahihin zabe
November 12, 2021Talla
Taron wanda Shugaba Emmanuel Macron na Faransan ya karbar bakuncinsa, ya yi wannan kiran ne cikin sanarwar bayan taron da suka kammala a birnin Paris, inda suka yi barazanar kakaba takunkumi ga duk wanda ya yi yunkurin yin kafar ungulu ga zaben na Libiya da za a gudanar ranar 24 ga watan Disamba mai zuwa. Libiya dai ta shiga halin tasku, tun bayan da kungiyar tsaro ta NATO ta jagoranci kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar marigayi Muammar Gaddafi a shekara ta 2011.