Saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Libiya
January 13, 2020Talla
A wannan Litinin manyan bangarorin da ke rikici da juna a kasar Libiya, sun saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Moscow na kasar Rasha, kamar yadda jami'an diflomasiyya ta kasar Rasha ta tabbatar. Kasashen Rasha da Turkiyya suka taimaka aka kulla yarjejeniyar. Tun a wannan Lahadi da ta gabata aka fara aikin da ita bisa wani matakin kawo karshen rikici da ya dagula kasar da ke yankin arewacin Afirka.
Yayin da a daya hannu kasar Jamus ta bayyana shirin daukan nauyin taro kan samar da zaman lafiya a kasar ta Libiya tsakanin bangarorin da ke rikicin a ranar 19 ga wannan wata na Janairu.