Leburori sun mutu a hatsarin gini a Indiya
August 1, 2023Talla
Firayim Ministan kasar Indiya Narendra Modi ya bayyana kaduwarsa kan hatsarin da ya yi sanadiyar rayuka, gwamnatinsa ta ba da umarnin biyan diyya ga iyalan ma'aikatan da suka mutu da wadan da suka jikkata a hatsarin.
Hatsari a manyan wuraren gine-ginen ababen more rayuwa sun zama ruwan dare a Indiya, ko a watan Oktoban 2022 mutane 130 sun mutu a Gujarat a lokacin da wata gada ta ruguje jim kadan bayan gyara ta.
A shekarar 2016, an samu asarar rai na mutum 26 a rugujewar wata gadar sama a kan wani titi mai cunkoson jama'a a Kolkata fadar gwamnatin jihar jihar Bengal da ke gabashin kasar Indiya.