Laurent Gbagbo zai gurfana a gaban kotun duniya ta ICC.
February 19, 2013Laurent Gbagbo ɗan shekarun 67 da haifuwa ana tuhumarsa da aikata man'yan laifukan guda huɗu, waɗanda suka haɗa da na kisan gilla da fayɗe, da kuma wasu laifukan a lokacin zaɓen da aka gudanar a shekarun 2010 zuwa 2011.
A ƙarshen zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar wanda a kansa ya ƙi amincewa da nasarar' da shugaba Alassane Ouattara ya samu a cikin watan Nuwanba shekara ta 2010.A wannan zama kotu zata yi ƙokarin tabbatar da shaidu har ɗari shidda ,na yin amfani da hanyoyin kisan gilla da tsohon shugaban ya riƙa yin amfani da su akan jama'a domin ci gaba da riƙe mulki.Idan kuma har hakan ya tabbata kotun zata tuhume shi da laifukan, kana ya fuskanci shari'a.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi.