1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Libiya na kara sukurkucewa

Suleiman Babayo MAB
January 5, 2020

Gwamnatin Libiya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya mai rike da birnin Tripoli ta ce dakarunta sun kai farmaki kan filin jirgin saman soja na mayakan sa kai.

https://p.dw.com/p/3VjXg
Libyen Kämpfe | Zerstörung nach Luftangriff
Hoto: picture-alliance/Photoshot

An ci gaba da kai ruwa rana tsakanin bangarorin da ba sa ga maciji da juna a rikicin kasar Libiya. Gwamnatin da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya mai rike da birnin Tripoli ta ce dakarunta sun kai farmaki kan filin jirgin saman soja na mayakan da ke biyayya ga Janar Khalifa Haftar kusa da iyaka da kasar Tuniya inda aka lalata makamai da tarwatasa mayakan sa kai.

Sai dai mai magana da yawun sojojin gwamnati bai yi karin haske bisa abin da ya faru lokacin farmakin.

Kusan mutane 30 suka halaka yayin da wasu da dama suka jikata sakamakon hari jiragen saman yaki a kudancin birnin Tripoli. Hukumomin kiwon lafiya sun ce lamarin ya faru lokacin aka kai harin kan makaranta, yayin artabu tsakanin bangarorin. Tuni MajalisarDinkin Duniya ta yi tir da harin kan makarantar. Rikicin na Libiya yana kara sukurkucewa duk da Turkiyya ta amince da tura dakarun domin taimakon gwamnatin da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.