1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lambar yabo ta Nobel ta Physics ta 2020

Abdullahi Tanko Bala
October 6, 2020

An bada lambar yabo ta Nobel ta 2020 ta kimiyyar lissafi wato Physics ga wasu masana kimiyya su uku da suka hada da Roger Penrose daga Birtaniya da Reinhard Genzel daga Jamus da kuma 'yar kasar Amirka  Andrea Ghez.

https://p.dw.com/p/3jWKV
Nobelpreis für Physik 2020 Roger Penrose, Reinhard Genzel, Andrea Ghez
Hoto: Niklas Elmehed for Nobel Media

Penrose farfesa ne a jami'ar Oxford yayin da Genzel yake shahararriyar cibiyar binciken kimiyya ta Max Planck a Jamus. Sai kuma Ghez wadda mai binciken kimiyya ce a jami'ar California.

Ghez dai ita ce mace ta hudu da suka sami lambar yabon a fannin kimiyar lissafi wato Physics a tsawon tarihi tun da aka fara bada lambar yabon.

Dukkan mutanen uku sun sami lambar yabon ce bisa aikin da suka gudanar na binciken tasirin nauyi a sararin samaniya da ake yiwa lakabi da black hole.