Lafiya Jari: WHO ta yi gardagadi kan Aspartame
August 11, 2023Miliyoyin mutane ke yin amfani da wannan sinadari na Aspartame a duniya kuma yana cikin samfuran abinci sama da dubu 6,000 wasu Amirkawa ne masu bincike suka gano sinadarin a shekara ta 1965.
Hukmar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi a kan sinadarin na Aspartame da ta ce yana da illa
Yawan amfanin da sinadarin wanda kan iya janyo cutar daji ko kansa sotari yakan fara da saka mutum cikin jinya ta rashin lafiya na wasu sasan jikinsa da kan iya tabuwa. Sautari dai mutane arha da rangwame ke kai su yin amfani da wannan sinadari saboda ganin tsadar suga watakilla sun gwammmace kashe kudin kadan domin biyan bukata. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin kan a yi taka tsan-tsan wajan amfani da sinadarin na Aspartame da ke kara dandano na zaki wanda ake yi wa sunan kafi suga.