1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An mayar da Rasha saniyar ware a harkokin wasanni

Lateefa Mustapha Ja'afar RGB
March 7, 2022

A karshen mako Manchester City ta yi wa 'yar uwarta ta United cin kaca kamar yadda Frankfurt ta bi Hertha Berlin har gida ta kuma yi mata dukan kawo wuka.

https://p.dw.com/p/488Rv
Russland Putin beim Judo-Training in Sotchi
Hukumar IJF ta soke duk wasu mukamai da ta bai wa PutinHoto: Mikhail Klimentyev/Sputnik Kremlin/AP/dpa/picture alliance

Hukumar Wasan Judo ta Duniya IJF ta kwace duk wani mukami da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da kuma wani hamshakin mai kudi Arkady Rotenberg suke da shi a hukumar. Koda yake ba a alakanta kwace mukaman da yakin da Rashan ke yi da Ukraine ba, a ranar 27 ga watan Fabarairun da ya gabata, hukumar ta IJF ta sanar da sauke Putin daga mukamin shugabancin girmamawa da ta ba shi sakamakon yakin.

Rotenberg yana rike da mukamin manajan ci-gaba na hukumar ta wasan Judo tun a shekara ta 2013. Hukumar ta IJF  ta kuma soke babban wasan da aka shirya gudanarwa a Rashan cikin watan Mayun wannan shekara. Haka kuma Hukumar Wasan Kokawa na Taekwondo ta kwace kyautar girmamawa da aka bai wa Putin din a shekara ta 2013 kana ita ma Hukumar Wasan Linkaya ta Duniya ta kwace kyautar da ta ba shi a 2014.

China | Beijing Paralympics | Eröffnungsfeier | Maksym Yarovyi
Ukraine na mataki na biyu a gasar masu bukata ta musamman Hoto: Andy Wong/AP Photo/picture alliance

Har wa yau a karshen mako 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na masu bukata ta musamman wato Paralympic na kasar Rasha suka koma gida, bayan da aka hana su fafatawa a gasar da ke gudana a yanzu haka a birnin Beijing na kasar Chaina a sakamakon hare-haren da Rasha ke kai wa a makwabciyarta Ukraine.

 A yanzu haka dai Chaina ce ke kan gaba a gasar ta Paralympics da lambobi 25. Zinare bakwai da azurfa takwas da kuma tagulla 10, yayin da Ukraine ke biye mata da lambobi takwas, zinare hudu da azurfa uku sai kuma tagulla daya. Kasar Kanada ce ke a matsayi na uku da lambobi 12, zinare hudu da azurfa biyu da kuma tagulla shida. Sai kuma Jamus a matsayi na takwas da lambobi takwas, zinare daya azurfa biyar da kuma tagulla biyu.

Hertha BSC - Eintracht Frankfurt
Farnkfurth ta lallasa Hertha da ci 4-1Hoto: Soeren Stache/dpa/picture alliance

A wasannin Bundesliga na Jamus kuwa, a wasannin da aka buga a mako na 25 an tashi wasa kunnen doki tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Bayern da takwararta ta Bayer Leverkussen da ci daya da daya, yayin da aka wasa Wolfsburg na da ci daya Union Berlin na nema. Ita ma dai Augsburg ta bi Arminia Belefield har gida ta kuma lallasa ta da ci daya mai ban haushi, haka Hoffenheim ta bi Cologne har gida ta caskara ta, da ci daya da nema. Ita kuwa Frankfurt ta yi wasan kura ne da Hertha Berlin, inda ta yi tattaki ta kuma caskara ta da ci hudu da daya.

A wasan da aka fafata tsakanin Bochum da takwararta Fürth kuwa, Bochum din ce ta samu nasara da ci biyu da daya, kana Stuttgart ta lallasa Borussia Mönchengladbach da ci uku da biyu. Sai kuma wasan da sashen Hausa na DW ya kawo muku tsaknin RB Lepzig da SC Freiburg, inda aka tashi wasa kunne doki daya da daya. Har yanzu, Bayern ce ke saman tebur da maki 59 yayin da Borussia Dortmund ke biye mata da maki 50 sai kuma Leverkussen a matsayi na uku da maki 45. 

BdTD | England
Yan wasan Manchester City sanye da riga mai launin tutar UkraineHoto: Oli Scarff/AFP/Getty Images

A gasar Premier League ta Ingila kuwa, Arsenal ta lallasa Watford da ci uku da biyu kana Liverpool ta samu nasara a kan Westham da ci daya mai ban haushi. Wasan da ya fi daukar hankali shi ne na Manchester City da takwararta ta United. Kuma United din ce ta sha kashi da ci hudu da daya. Wannan shan kayen dai, na kara nesanta United din da gasar cin kofin kwallon kafa na zakarun Turai in har ba ta yi kokarin tabuka abin azo a gani a wasanninta na gaba ba. A yanzu haka dai  Manchester City ce ke saman tebur da maki 69, yayin da Liverpool ke biye mata da maki 63 sai kuma Chelsea a matsayi na uku da maki 53.

Al’amura sun tasamma tabarbarewa kungiyar kwallon kafa ta Kano pillars wacce a yanzu ta fado kasan tebur har ya zama tana daf da fadawa ajin gajiyayyu, masu fashin baki kan harkokin wasanni na danganta wannan matsala da sakacin mahukuntan kulob din da ma halin ko in kula da ake nunawa lamarin da suke ganin matukar ba an yi wa tufkar hanci ba, kunngiyar za ta fada yanayin ni yasun da za ta dade bata fito ba.