1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Labarin Wasanni 26.09.2022

Suleiman Babayo RGB
September 26, 2022

Eliud Kipchoge na kasar Kenya ya lashe zinare biyu a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya a yayin da fitacaccen dan wasan Tennis Roger Federer ya sanar da yin ritaya daga wasan.

https://p.dw.com/p/4HMtg
Eliud Kipchoge gewinnt Berlin Marathon
Hoto: Fabrizio Bensch/REUTERS

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana cewa, an samu inganta yanayin da ma'aikata 'yan kasashe ketere ke aiki a kasar Katar wadanda suke aikin gina wuraren da za a yi amfani da su a lokacin wasan cin kofin kwallon kafa na duniya a karshen wannan shekara ta 2022. Shugaban gwamnatin na Jamus ya fadi hakan ne a yayin ziyararsa a kasar ta Katar. Tuni hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Jamus ta yi alkawarin cewa 'yan wasan kasar, za su samu karin kyautar kudi na Euro 400,000 muddun suka lashe kofin na duniya a karshen wannan shekara.

Katar | Replika des FIFA WM Pokal vor der Skyline von Doha
Kofin kwallon kafa na duniya 2022Hoto: Ulmer/IMAGO

Karkashin yarjejeniya tsakanin hukumar kula da wasan kwallon kafar ta Jamus da 'yan wasa, an amince, 'yan wasan za su samu Euro 50,000 inda suka samu nasara a wasannin rukuni, sannan Euro 100,000 a wasan kusa da na kusa da na karshe, kana Euro 150,000 a wasan kusa da na karshe, in da kuma matsayi na uku suka samu, za su samu Euro 200,000. Idan sun kai wasan karshe suna da Euro 250,000. Idan kuma Jamus ta lashe gasar 'yan wasan za su samu kudin da ya kai Euro 400,000.

Eliud Kipchoge dan kasar Kenya wanda ya lashe zinare biyu a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya, ya kafa sabon tarihi a wannan Lahadi da ta gabata a birnin Berlin na Jamus, inda ya kammala gudun fanfalaki cikin sa'oi 2 da minti 1, da dakika 9 da motsi. Yanzu haka ya kafa tahiri inda ya zarce gudunsa na baya da kasa da dakikoki 30. A wannan gudu na birnin Berlin na Jamus, 'yar kasar Habasha Tigist Assefa ta yi ba-za-ta wajen lashe gudun mata cikin sa'oi 2 da mintoci 15 da dakika 37.

Laver Cup 2022 - Tennis-Abschied von Roger Federer
Roger Federer ya yi ritaya daga TennisHoto: Andrew Boyers/Reuters

Daya daga cikin shahararrun 'yan wasan tennis na duniya, Roger Federer daga kasar Switzerland ya yi ritaya daga wasan. Dan shekaru 41 da haihuwa ya shafe fiye da shekaru 20 ana fafatawa da shi a fagen tennis na duniya. Shi dai Roger Federer a tsawon shekaru ya samu nasarar lashe gasar US Open fiye da 20 kuma yana cikin 'yan wasan tennis da suka yi fice a duniya.

Kasar Masar ta bayyana aniyar neman ganin ta dauki nauyin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya wato Olympics na shekara ta 2036. Ministan wasan kasar Ashraf Sobhi ya bayyana haka a karshen mako, a lokacin da ya karbi makuncin shugaban hukumar Olympics ta duniya, Thomas Bach wanda ya kai ziyara birnin Alkahira fadar gwamnatin kasar ta Masar. Muddun kasar ta Masar ta samu wannan nasara kan daukar nauyin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya a shekara ta 2036 za ta zama kasar Larabawa ta farko da ta samu irin dama.

To bayan dakatarwa na tsawon shekaru biyu, saboda annobar cutar Covid-19 a karshen mako aka gudanar da wasannin kwallon kafa na DW na sassan Afirka kuma a wannan shekara sashen Turancin Ingilishi na Afirka da ake kira Africa-Link ya samu nasarar lashe wannan wasa na sassan Afirka na tashar DW.

Ana ci gaba da wasan mata na duniya na kwallon kwando da ke wakana a kasar Australiya, sai kasar Mali wakilayar Afirka a gasar ta sha kaye a hannun mai masaukin baki.