1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Labaran Afirka masu daukar hankali a Jamus

Abdourahamane Hassane ZMA
June 7, 2024

Yajin aiki na gama gari kan bukatar karin albashi a Najeriya, da zaben kasa baki daya a Afirka ta Kudu su ne manyan batutuwa da jaridun suka yi sharhi a kai.

https://p.dw.com/p/4gnql
Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Za mu yaye kallabin shirin na wannan makon ne da labarin da jaridar die Tageszeitung ta wallafa mai taken "Duk mai aiki ya kamata ya ci abinci". Bayan yajin aikin gama-gari na kwanaki biyu, gwamnatin Najeriya ta amince ta tattaunawa da 'yan kwadago.

Kungiyoyin kadago na NLC da TUC sun sa gari ya yi tsit, ba shiga ba fita, inda kowa ya tsaya gidansa saboda yajin aikin ma'aikata na neman  karin al bashi.

Akwai dalilai guda biyu na yajin aikin domin neman karin albashin. Rayuwa ta yi tsada amma cikin haka gwamnatin ta yi karin kudade na wutar lantarki ga abubuwan sun dame wa kasar.'Yan kwadagon na ganin a kan haka babu hujja su cigaba da karbar Naira dubu 30 kwatankwanci (Euro 18) matsayin kudin albashi mafi kankanta a Najeriya sun ce sai gwamnatin ta ba su Naira kusan Naira 500 kimanin Euro 300.

Nigeria | NLC Protest
Hoto: Nasir Salisu Zango

Faduwar darajar takardar kudin Najeriya wato Naira da tsadar Dalar Amirka da hauhawar farashin kayayyaki da rashin gazawar kasafin kudi da kara asarar kudaden lamuni wadannan dukkaninsu wasu abubuwa ne da suke hana ruwa gudu a Najeriyar a cewar Jaridar Die Welt wacce ta ce jama'a sun gaji.

Faduwar jam'iyar ANC a zaben Afirka ta Kudu zai zama wata sila na shigar kasar cikin rudani na dindindin wanda ake da fargaba farar fata za su iya fuskantar bita da kulli na amshe gonakinsu da filaye da korar baki, wannan shi ne abin da ake yin  kus-kus a kansa a game da  rashin nasara jamiyyar  ANC a zaben na Afirka ta Kudu wannan shi ne taken da jaridar Frankfuter Allgmeine ta wallafa a game da wannan dambarwa.

Südafrika I Wahl
Hoto: Jerome Delay/AP/picture alliance

Rinjaye ya bata  saboda jam'iyar ANC ta gaza samun kaso 50 na kuri'u cikn 100, yanzu dole sai ta tsaida ruwan miya da sauran jam'iyyun siyasa domin kafa gwamnati, yanzu sai abin aka ce mata ba abinda ta ce ba, a cewar jaridar Welt Plus.Ta ce  ANC na rike da kashi 40.24 na kuri'u, da yawan 'yan majalisa 159 sabanin a baya da suke da 230.

Sai jam'iyyar DA (Democratic Alliance) wadda ke da  kashi 21.74 da kujeru 87, sai sabuwar jamiyar Zuma ta MK wacce ita ce ta uku kuma raba-gardama. Shin ko za ta goyi bayan ANC ayyar tambayar kenan da jaridar Die Welt Online ta aza. Babu tabbas a cewar Frankfuter Allgmeine saboda kiyayyar da ke tsakanin Zuma da ANC wanda suka yi sanadin daureshi a gidan kurkuku.

Südafrika Präsident Cyril Ramaphosa nach der Wahl
Hoto: Kyodo/picture alliance

Karawa tsakanin Ramaphosa da Jacob Zuma, yakin shekaru 30 na Afirka ta Kudu wannan shi ne taken labarin da jaridar Online zeitung  ta wallafa a shafinta na farko  kan cewar, tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata, fafatawa tsakanin 'yan siyasar biyu mafi dadewa a kasar ta mamaye siyasar Afirka ta Kudu. Jacob Zuma ya sha alwashin sai ya dauki fansa game da irin wulankanci da ya fuskanta saboda yanzu dole a neme shi domin yin kawance.