Kokarin kulla dangantar Turai da Afirka
January 20, 2023Za mu fara sharhunan ne da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wacce ta duba yunkurin ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock na kara kusancin dangantakar Jamus da Afirka. Jaridar ta ce wata kila yakin Ukraine da Rasha yana daga abin da ya ingiza ministar neman karin hulda da Afirka, inda yanzu haka a kungiyance, tarayyar Turai kanta na neman hadin gwiwar Turai da Afirka a kungiyance.
A ziyarar da ta kai shelkwatar tarayyar Afirka a birnin Addis Ababa, ta ce harin da Rasha ta kai wa Ukraine ta kaiwa dukkan duniya ne ba Turai kadai ba. Tana mai cewa Afirka da Amirka da tarayyar Turai duk sun tsaya ne kan abu gudu, wato kare hakkin dan Adam, samar da tsaro da ci gaban tattalin arziki.
A yanzu dai duniya na neman hadin kai yana da mahimmanci saboda rikice-rikice sun yadu, daga yakin Rasha na zalunci, matsalar sauyin yanayi zuwa karancin abinci. Jaridar na mai cewa ministar harkokin wajen ta ce za mu iya magance wadannan rikice-rikice kawai in mun yi aiki tare.
Za mu dora da jaridar Neue Zürcher Zeitung, wacce ta ce me ya sa Majalisar Dinkin Duniya ba ta ayyana yunwa a Somaliya duk kuwa da cewar dubban mutane na fuskantar yunwa ba? Jaridar ta ce watakila masu lura da al'amura da dama na ganin rashin son yin kuskure ne idan aka yi la'akari da halin da ake ciki na yunwa a yanzu, mutum zai ce a'a, hujjar da ba za a iya gamsuwa da ita ba.
Domin ko dai akwai yunwar ko babu ita amma yin gum ba amsa ba ce. Jaridar ta ce yunwa bai kamata a maida ita siyasa ba kuma ba. Rikicin ya shafi yankin kusurwar Afirka a halin yanzu ana fama da fari mafi muni shekaru a 40 da suka gabata. Yanzu dai an samu shekaru biyar a jere damina ba ta isa kamar yadda ake bukata ba, inda miliyoyin mutane ba sa samun abinci isasshe. A yanzu jama'a na ta gudun hijira don neman tsira daga wannan yunwar.
A sharhinta jaridar Berliner Zeitung, ta ce rikicin da aka manta da shi a Afirka. Angola kusan kafafen yada labarai da yan siyasa sun yi watsi da ita. Wannan yana daga cikin manyan labarai goma da aka yi watsi da su a cikin rikice-rikice na bara a cewar wani bincike kan Afirka. Wani rahoto da kungiyar "Breaking the Silence" kungiyar agajin kare hakkin wadanda aka manta da su ta yi bisa kafofin yada labarai kan fari a Angola.
A cewar kungiyar kusan mutane miliyan daya da rabi ba su samu wadataccen abinci ba a bara musamman a Kudu maso Yammacin kasar ta Angola. Jaridar ta ce kafofin yada labarai na watsi da irin wannan yananyi, inda a bincike suka gano kafofin yada labarai sun yi labarin na Fari a Angola sau 1800, yayinda in an kwantat d bikin bude gasar wasannin Olympics a birnin Beijing an buga labarai masu kyau har 285,000.
Jaridar die Tageszeitung kuwa ta duba kan rashin wutar lantarki a kasashen kudancin Afirka. Jaridar na mai cewa tun tsawon lokaci kasashen na fuskantar matsalar, to sai dai yanzu ikirarin rashin wuta ya yi muni sakamakon canjin yanayi. Misali a kasar Zambiya daga Lusaka babban birnin kasar har izuwa tsakiyar ana fuskantar matsalar, inda ake daukar Zambiya a matsayin tsibiri na haske a cikin tekun duhu. Zambiya ce ke samar da wutar lantarki fiye da yadda ake sha kuma ta samu kudi ta hanyar fitar da shi zuwa kasashe makwabta, wadanda suke da karancin wutar lantarki.