Mutane biyu sun lashe kyautar Nobel
October 5, 2018Dr Denis Mukwege ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare wadanda aka ci zarafinsu yayin da Nadia Murad ta bayyanawa duniya irin yadda ta dandana kudarta a hannun 'yan ta'addan kungiyar IS. A lokacin mika musu wannan kyauta dai, kwamitin bayar da kyautar ya bayyana Dr Denis a matsayin jajirtacce wanda ya dade yana sukar gwamnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da sauran kasashe kan rashin daukar matakin kawo karshen cin zarafin mata a matsayin makamin yaki, yayin da Nadia Murad ta kasance cikin mata 3,000 'yan kabilar Yazidi wadanda kungiyar IS ta yi awon gaba da su, kafin ta yi nasarar tserewa bayan watanni uku. Nadia dai ta rubuta littafi kan halin da ta tsinci kanta yayin da take hannun 'yan IS din. Tuni dai gwamnatin kasar Kwango ta taya Dr Denis murna kan wannan ci-gaba da ya samu a rayuwarsa.