1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyautar zaman lafiya ta Nobel

Usman Shehu Usman AA
October 9, 2018

Fitaccen likitan mata mai suna Dakta Denis Mukwege dan kasar Kwango, da Nadia Murad sun samu kyautar zaman lafiya ta Nobel ta bana. Wanda ya yi suna a duniya bisa tallafa wa matan da aka yi wa fyade a Kwango.

https://p.dw.com/p/364PB
Bildkombo, Bildcombo  Dominique Gutekunst Denis Mukwege und Nadia Murad, Friedens-Nobelpreis 2018

Ya samu kyautar ne, tare da fitacciyar ´yar fafutikar kare hakkin jama'a mai suna Nadia Murad, wacce ta shahara wajen kare kabilar Yazidi, da ita kanta ta taba samun kanta cikin wadanda aka yiwa fyade.

Heiko Maas, ministan harkokin wajen kasar Jamus, wanda shima ya mayar da martani kan wannan kyautar ta Nobel da aka bayar, a jerin martanonin da aka samu a fadin duniya, ya ce wajibi ne kasashen duniya su cigaba da daukar matakan da suka dace dan kare mata daga shiga hatsura. Sai shima babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya maida martani inda yake cewa:

 ''Kwamitin bada kyautar Nobel ya lura da kokarin Nadia Murad da Denis Mukwenge, a matsayin masu bada gudumawarsu wajen zaman lafiya. Karramasu da aka yi, ya nuna cewa ba a manta da masu fama da matsaloli ba wadanda ba a san iya adadinsu ba, masu fuskantar tsangwama da kyara da suke a boye, da aka manta da su.

A kyautar Nobel da aka basu, wadanana mutanen biyu za su raba dalar Amirka miliyan daya. wace za a mika musu ranar 10 ga watan disamba a Osla babban birnin kasar Norway.

Ku saurari ragowar muryoyin wadanda aka yi hira da su, a cikin rahotan namu.