1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abiy Ahmed ya karbi Kyautar Nobel

Jane Nyingi Zipporah Nyambura, LMJ
December 10, 2019

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya karbi kyautar zaman lafiya ta Nobel a birnin Oslo na kasar Norway, a wani taro da ya hada al'ummomin kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/3UZ0G
Norwegen l Verleihung des Friedensnobelpreis an Abiy Ahmed in Oslo
An mika kyautar zaman lafiya ta Nobel ta bana ga Firaministan Habasha Abiy AhmedHoto: picture alliance/dpa/NTB scanpix/H. M. Larsen

Da yake jawabi jim kadan bayan da ya karbi kyautar a birnin Oslo na kasar Norway cikin wani kasaitaccen biki, Firaminista Abiy Ahmed bai ji nauyin bayyana abin da ya kira da zaman lafiyan da ba shi da tabbas a Afirka ba. Abiy dai ya yi zargin cewa tasirin sojojin kasa da kasa da kasasshen da ke da karfin fada aji a duniya da kuma kungiyoyin 'yan ta'adda ne ke da laifi wajen karuwar rikice-rikice a yankin kahon Afirka. Sai dai duk da ya lashe kyautar ta Nobel, har yanzu al'ummar Habashan ba su gamsu da salon mulkin Abiy ba, domin kuwa yana shan suka.

Äthiopien Addis Abeba Anhänger vor dem Haus des Oppositionsführers Jawar Mohammed
Zanga-zangar adawa da salon mulkin Abiy na zaman babban kalubalensa a gida HabashaHoto: picture-alliance/AP Photo/M. Ayene

An zargi gwamnatinsa da kokarin murkushe masu zanga-zangar adawa da salon mulkin Abiy da karfin tuwo. Zanga-zangar dai ta barke ne bayan da wani da ya yi fice wajen sukar salon mukin na Abiy ya yi zargin cewa jami'an 'yan sanda sun ci zarafinsa kan hakan. Haka kuma an soki matakin kin amsa tambayoyin 'yan jarida bayan da ya karbi kyautar zaman lafiyar ta Nobel a birnin Oslo da Abiy ya dauka. Tun dai a shekara ta 2018 Abiy ya samu yabo, bayan da ya kaddamar da gagarumin gyara a fannin tattalin arziki da siyasa a kasar. Abiy dai ya saki firsinonin siyasa da masu fafutuka tare kuma da dage haramcin da aka yi wa wasu jam'iyyun siyasa a kasar. Firaministan Habashan Abiy Ahmed dai na zaman mutum na 10 daga nahiyar Afirka da ya lashe kyautar zaman lafiyar ta Nobel, kuma mafi karancin shekaru. A shekara ta 1960 ne dai Albert John Luthuli dan siyasar kasar Afirka ta Kudu ya lashe kyautar zaman lafiyar ta Nobel, a karon farko da kyautar ta isa nahiyar Afirkan.