1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwararar danyan mai a Niger Delta

September 9, 2013

Kamfanin mai na Shell na tattauna batun biyan diyya ga al'ummomin kauyukan da kwararar danyan mai ta shafa a yankin Niger Delta da ke Tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/19eGj
Hoto: picture alliance/dpa

Shekaru biyar bayan da aka samu kwararar danyan man fetur da aka bayyana da mafi muni a yankin Niger Delta a Tarayyar Najeriya, jami'an kamfanin mai na Shell sun fara tatauna batun biyan diyya da kuma kwashe dagwalon danyan man fetur din.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an kamfanin na Shell na tattaunawa ne da wakilan kabilar Bodo a kudancin garin Fatakwal, domin tattauna batun da shugabannin kabilar ta Bodo suka sha alwashin yin matsin lamba ga kamfanin na Shell, domin samarwa da al'ummar yankin mafita da kuma fatan kawo karshen gurbatar muhalli a yankin na Nija Delta.

Kwararru sun bayyana cewa kwararar danyan man fetur din da ta faro tun a shekara ta 2008, ta haddasa asarar dukiyoyi da dama yayin da ta shafi kimanin mazauna yankin dubu 30.

A cewar wani kamfani mai fafutukar kare hakkin dan Adam mai suna Leigh Day, da ke wakiltar kimanin mutane dubu 15 da abin ya shafa, ya ce tun daga shekara ta 2008 din kawo yanzu al'ummar yankin na zaune ne cikin dagwalon danyan man fetur din ba tare da an kawo musu wani dauki ba.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Auwal Balarabe