1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamitin Red Cross na son kai agaji Yemen

Yusuf BalaApril 4, 2015

Masu aikin agaji dai a ranar Talata da ta gabata sun zargi mahukuntan na Saudiyya da sojojin ƙawancensu bisa hana musu damar kai waɗannan kayan agaji.

https://p.dw.com/p/1F2hY
Deutes Rotes Kreuz (DRK)
Hoto: picture alliance/blickwinkel/McPHOTOs

Kwamitin agajin ƙasa da ƙasa na Red Cross ya bayyana a ranar Asabar din nan cewar har yanzu akwai jiragen ruwa ɗauke da kayan agaji da magunguna da ma'aikata da ke dakon a shigar da su Yemen duk kuwa da kiraye -kiraye ga sojojin ƙawance bisa jagorancin Saudiyya na su bada dama kasancewar suke da iko da iyakokin ruwa dama samaniyar ƙasar ta Yemen.

Shi dai wannan kwamiti na ICRC na buƙata ne a ba shi tabbacin kariya ta yadda zai samu ya tura jirage biyu zuwa birnin na Sanaa ɗaya maƙare da kayan magunguna da za a duba marasa lafiya sama da dubu ɗaya, yayin da a ɓangare guda kuma akwai tan 30 na wasu kayan magungunan da kula da tsaftar ruwan sha haka zalika da ma wani jirgin da zai ɗauki jami'an lafiya zuwa birnin Aden.

 

Masu aikin agaji dai a ranar Talata da ta gabata sun zargi mahukuntan na Saudiyya da sojojin kawancensu bisa hana musu damar kai wadannan kayan agaji sakamakon fadan da aka shiga tsawon kwanaki 10 a kokarin ganin bayan mayakan Houthi.