SiyasaAfirka
Kwalara ta hallaka mutane a Habasha
November 30, 2023Talla
Akalla mutane 23 ne rahotanni ke cewa cutar kwalara ta yi ajalinsu a gabashin kasar Habasha, yankin da ya fuskanci ambaliyar ruwa a baya-bayan nan.
Kungiyar taimako da kare hakkin kananan yara ta Save the Children wadda ta ba da alkaluman wadanda suka mutun, ta ce akwai yiwuwar cutar ka iya bazuwa zuwa wurare da dama a yankin.
Kasar ta Habasha da ke makwabtaka da Kenya da Somaliya, sun fuskanci ruwan sama kamar da bakin masaki da ya haddasa ambaliyar da ta yi sanadin salwatar rayuka a yankin kusuwar Afirka.
Save the Children din ta kuma ce cikin makonni biyu da suka gabata, akwai mutum 772 da suka kamu, kuma 23n suka mutu.