Kuri'ar jin ra'ayin makomar yankin Darfur
April 11, 2016Shugaban kasar Omar al-Bashir wanda kotun ICC ta ke nema ruwa a jallo a bisa laifuffukan yaki ya jaddada cewar duk da halin da ake ciki a yankin, za a cig aba da kada kuri’ar neman jin ra’ayin jama’ar a kan ko zasu hade da sauran jihohi 5 don zama yanki guda ko kuma zasu ci gaba da zama a matsayinsu.
To sai dai a hannu daya, kungiyoyin ‘yan tawaye sun kaurace wa shirin a inda suka bayyana cewar babu kamshin adalci a ciki. Ita ma kasar Amirka a nata bangaren cewar ta yi muddin kuri'ar ta gudana a karkashin jagorancin shugaba Omar al-Bashir, akwai alamar tambaya a kan sahihancin zaben.
Tun dai a shekara 2003 al’ummar yankin ke ta fafutukar samun 'yancin gashin kansu daga hannun gwamnatin Sudan a inda suke cin karo da turjiya daga hukumomin kasar.