Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna CDU na gaban SPD
September 3, 2017Kuri'ar jin ra'ayin jama'a dai ta nunar da jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya ta Angela Merkel ta sha gaban 'yan Social Democrat a zaben da za a yi na 'yan majalisa a jihar da ke zama fitacciya a nan Jamus North Rhine-Westphalia a ranar Lahadi.
A kididdigar da shirin YouGov na kafar yada labaran Sat.1 ya fitar ya nunar da cewa jam'iyyar CDU na da goyon baya na kashe 31 cikin dari yayin da jam'iyyar SPD ke da kashi 30 cikin dari.
Wadanda ke bibiyar wannan kididdiga dai sun ga kari na kashi hudu cikin dari ga jam'iyyar ta CDU idan aka kwatanta da makonni biyu da suka gabata, wannan kuma ya nuna cewa jam'iyyar SPD ta ga koma baya na maki shida. Martin Schulz dai na da kalubale na jam'iyyarsa ta SPD ta samu tagomashi a zaben 'yan majalisar jihar North Rhine-Westphalia domin samun daidaito a shirinsa na kalubalantar Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a zaben gama gari ranar 24 ga watan Satimba.
Zaben wannan jiha dai na taka muhimmiyar rawa a zaben tarayya a nan Jamus.