1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kura ta lafa a birnin Maiduguri

Amin Suleiman MohammadJanuary 26, 2015

An dage dokar hana fita da aka kafa a garin Maiduguri fadar gwamnatin Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya

https://p.dw.com/p/1EQXv
Nigeria Maiduguri Militär Sicherheit Anti Boko Haram 2014
Hoto: picture-alliance/epa

Kura ta lafa a birnin Maiduguri bayan mummunan harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai da nufin karbe garin a jiya inda rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da kawo karshen doka hana fita ta ba dare ba rana da aka kafa.

Hankula sun tashi inda ciki ya kada matuka bayan yunkuri da 'yan Kungiyar Jama'atu Ahlulu Sunna da aka fi sani da Boko Haram wanda aka bayyana da shi ne mafi girma na shiga domin karbe iko da Maiduguri fadar tsohuwar helkwatar jihar Arewa maso Gabas.

Nigeria Traditionelle Jäger Anti Boko Haram Kämpfer
Hoto: Reuters/Joe Penney

Rahotanni sun nuna cewa an samu hasarar rayuka da dama a dukkanin bangarorin da kuma fararen hula inda yawancin mazauna unguwannin da ke bayan garin suka tsere zuwa garin wanda dama yake mafaka da dubun-dubatar 'yan gudun hijira da sassan jihar. Ya zuwa yanzu dai babu cikakkun alkaluma na yawan wadan da fadan ya rutsa da su inda ake cewa an hallaka ‘yan kungiyar Boko Haram sama da 200 da kuma jami'an tsaro da fararen hula.

Jami'an tsaro sun sanar da janye dokar hana fita ta ba dare ba rana da aka sanya a garin bayan kura ta lafa. Tuni jama'ar garin Maiduguri suka fita domin ci gaba da yin harkokin su na yau da kullum inda mutanen unguwanni da ke kusa da wurin da aka gwabza fada tsakanin jami'an tsaron Najeriya da kungiyar suka fara komawa gidajensu.

Sai dai bayanai sun tabbatar da cewa kungiyar ta karbe iko da garin Munguno wanda shi ne gari mafi girma a yankin Arewacin jihar Borno inda ake fargabar ana garkuwa da daruruwan mutane ciki har da iyalan sojojin da ke barikin garin. Gwamnan Jihar Borno Kashim Shetima ya tabbatar da fadawar garin Munguno hannun ‘yan kungiyar inda ya bayyana abin da ya faru a munguno a matsayin abin tashin hankali da ba zai iya misaltuwa ba.

Anschlag in Maiduguri Nigeria Archiv Juli 2014
Hoto: AFP/Getty Images

Hare-hare dai na zuwa ne sa'oi 12 bayan shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kamala ziyarar yakin neman zabe a Maiduguri inda ya yi alwashin cewa in aka sake zabensa zai kawo karshen tashin-tashinar da ta addabi yankin cikin kankanin lokaci.