An tabo bakin haure 50 daga Sahara
September 13, 2022Talla
Kungiyar kula da kaurar jama'a IOM ta ce galibi wadanda aka ceto sun bata ne a yayin da suke kokarin dawowa daga Libiya, ko da yake hukumar ta ce akwai kuma wasu kuwa da ke kan hanyar shiga kasar Libiyar ta barauniyar hanya.
Mutane 49 daga cikin 50 din da aka ceta bayan sun makale a hamadar yankin Dirkou 'yan Najeriya ne, sai kuma wani mutun dan Kamaru daya in ji hukumar IOM.
Yanzu haka mutanen na samun kulawa daga mahukuntan yankin Agadez da ke arewacin Nijar tare da tallafin hukumar ta IOM.