1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar AI ta zargi sojojin Najeriya da laifin kisan gilla

October 18, 2013

Halin da yan gudun hijira suke fuskanta a gabar tekun Lampedusa da taron kolin kasashen Afirka kan kotun ICC sun dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako

https://p.dw.com/p/1A29y
Hoto: Getty Images/AFP

Kusan jaridun na Jamus gaba daya sun duba rahoton kungiyar kare hakkin yan Adam ta Amnesty International, game da kisan gilla ga daruruwan mutanen dake tsare a Najeriya bisa zarginsu da kasancewa yan kungiyar nan ta Boko Haram. Jaridar Neue Zürcher Zeitung tayi sharhi kan abin dfa ta kira, aiyukan rashin imani na sojoji a Najeriya inda kungiyar Amnesty tayi mummunan suka a game da kisan mutanen da aka tsare bisa fakewa da dokar ta-baci saboda zarginsu da laifin kasancewa yan kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar ta Najeriya. Amnesty a rahoton da ta gabatar a London a farkon mako, tace akalla mutane 950 ne sojoji suka kashe, yawancin su yayin da suke tsare a gidajen kurkuku na kasar, wasu kuma suka mutu saboda rashin kula ko saboda fama da cutuka. Kungiyar tace kisan na rashin imani kan wadanda ake tuhumarsu da kasancewa 'ya'yan kungiyar Boko Haram ya fi aukuwa ne a gidajen kurkukun soja a garuruwan Maiduguri dake jiharBorno da kuma Damaturu a jihar Yobe.

Labarin kungiyar Amnesty a game da kisan gilla da sojojin Najeriya ke aikatawa kan farar hula, yazo ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen karrama wasu shugabannin addinai biyu daga kasar, wato Limamin Kirista James Wuye da Imam Mohammed Ashafa na kungiyar nan ta neman sulhunta addanai a Nijeriya mai mazauninta a Kaduna. Jaridar Kölner Stadt Anzeiger ta rawaito cewar mutanen biyu za'a karramasu ne da lamba ta musamman ta zaman lafiya ta jihar Hesse a nan Jamus ranar 30 ga wannan watan na Oktoba. Jaridar ta dan tabo tarihin haduwar wadannan shugabannin addini biyu, inda tace bayan ko wanne daga cikin su yayi fama da wahaloli na tashe-tashen hankulan addini a kasar, sun hadu karon farko a watan Mayu na shekara ta 1995, inda suka yanke shawarar kafa kungiyar neman sulhunta addinai, wadda tayi tasiri matuka musamman a jihar Kaduna. Cibiyar bayar la lambar ta zaman lafiya ta Hesse, inji jaridar Kölnr Stadt Anzeiger, ta gamsu matuka da aiyukan wadannan mutane biyu, inda ma a karon farko ta yanke shawarar zaben mutane biyu domin karbar lambar ta Hesse.

Jaridun na Jamus sun kuma maida hankali kan taron koli na musamman da shugabannin kasashen Afirka suka yi a karshen makon jiya, inda suka duba yiwuwar janye kasashensu daga kotun kasa da kasa wato ICC a birnin The Hague, dake shari'armjasu aikata manyan laifuka. Jaridar Tagesspiegel tace ko da shike taron bai goyi bayan dakatar da wakilcin kasashen Afrika daga kotun ICC ba, amma shugabannin sun daidaita a kan cewar ba zasu sake bari kotun ta rika nema ko yiwa shugabannin Afirka dake kan mulki shari'a ba. Wannan kira ya biyo shari'a dake gudana a gaban kotun ta kasa da kasa a birnin Hagu ta shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto. Wasu daga cikin shugabannin kasashen na Afirka sun yi korafin cewar kotun na ICC aiyukan sa sun danganci wariya, saboda yafi maida hankali ga neman hukunta shugabanni daga nahiyar Afrika.

Kenia Prozess gegen William Ruto in Den Haag
Mataimakin shugaban Kenya William Ruto(dama) gaban kotun kasa da kasa ta ICCHoto: Reuters

A karshe jaridar Der Freitag tayi sharhi a game da halin da dimbin yan gudun hijira suke ci gaba da kasancewa a ciki a kusa da gabar ruwan Lampedusa na Italiya. Jaridar tace kasashen da yan gudun suke fitowa daga cikinsu suna rasa rayukansu a cikin teku,babu abin da ya dame su da makomar wadannan yan gudun hijira. Bayan mutuwar mutane fiye da 300 a farkon wannan wata, wasu arba'in sun ake rasa ransu lokacin wani dan karamin kwale-kwalen da suke ciki farkon wannan mako. Yayin da duniya take juyayin wadannan mutane dake rasa rayukansu kan hanyar neman rayuwa mai armashi a kasashen yamma, kasashen da suka fito daga Afirka suna ci gaba da nuna rashin damuwa. Ba kunya ba tsoron Allah, inji jaridar Der Freitag.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Mouhamadou Awal