Kungiya matasa mai bada tallafin ilimi
December 5, 2017Tallafin wadannan matasa dai yakan tabo bangarori daban daban na fannin ilmi a cewar Aliyu Haruna Daura da ke kula da sashen mulki da kudi na kungiyar;
"A bangaren ilmi mukan ba yara tallafin karatu a makarantun gaba da sakandare wasu kuma mukan basu kudade bakin iyakar abunda ka rubuta mana. Mukan duba muga asusun kungiya sai mu tallafa maka kuma masu karatun gaba da sakandare ne muke wa wannan tallafin".
"Su kuma 'yan frimary da sakandare muna basu tallafi ne ta hanyar yin aiki misali kwanan nan a karamar hukumar Mai'aduwa an kawo masu kayan kwajin kimiya wanda gwamnatin tarayya ta zabi jihar katsina kuma aka zabi wannan karamar hukumar aka zabi wata makarantar frimari. To sai aka kawo mana koke cewa wannan makarantar ba ta da ajin dakin gwaje gwajen inda nan da nan muka je muka gina masu dakin".