Koyawa yara yin tanadi don gobe
December 13, 2017Da yawa daga cikin yara 'yan makatun firamare kenan ke shewa cikin yanayi na farin ciki yayin da maluman su suka shiga fili da ke kewaye da tantina cikin rawa. yanayin da ke zama masomar fara wani shiri da a ka yi wa taken ''Koin Dream Challenge'' da ake gudanarwa a wani waje mai suna Moonland Garden da ke Kampala babban birnin kasar Uganda.
Shirin dai wanda a aka kaddamar a shekarar da ta gabata wani shiri ne na wata kungiya mai suna Iprofile, cibiya da ke gudanar da aikin ta badan riba ba wacce kuma ta kware wajen koyar da harkokin karfafa yara kanana da koyar da su ilimin harkokin kudi da na kananan sana'o'i dama sanin makamar shugabanci. Ai'sha Ali yar shekaru 23 da ke jagorancin wannan shiri dai ta bayyana cewa ta koyi ilimin harkokin kudi ne daga wajan mahaifinta.
Da taimakon wasu abokanta, Ai'sha ta yi nasarar koyar da yara 450 daga makarantun firamare 13 tun shekara da ta gabata. Ganin cewa da yawa daga cikin yaran sun fito ne daga iyalai marasa karfin tattalin arziki, shirin na Koin Dream Challenge na koyar da yaran yadda za su hada abun wuya da na hannu na adon mata wanda kuma suke sayarwa 'yanuwa da abokan arziki. Ana kuma koya musu yadda za su adana kudaden cikin dan karamin asusunan da ake kerawa na yara.
Bayan watanni biyu ko uku yaran daga makarantu da dama na bude asusun nasu inda ake bude musu asusun ajiya a bankuna da abinda da suka tara, kana wanda yafi tara kudi daga ciikin yaran ake zaben sa a matasayin zakara kuma jakadan shirin da Koin Dream Challenge. Reina Asimwe ita ta yi nasarar lashe gasar ta bara inda ta samu Shilin miliyan daya na Uganda wato kimanin dalar Amirka 275 wanda ta ke fatan amfani da shi wajen cimma burinta a rayuwa.