Koyar da karatu kyauta a Katsina
January 9, 2018Wadan nan malamai kimanin 170 dai da ke bada wannan gudumawa sun kunshi maza da mata dan hakane waki8lin DW a Katsina ya ji ta baki Amadu Sule Bagiwa wanda ya yi magana a madadin malamai maza " Da yawan mu mun yi shawara in muka je zamu dauki azuzuwan firamare 1, 2, 3. In aka ce harkar koyo da koyarwa ne inka dauki wannan sabon ginin ka ba shi harsashi mai kyau, to in suka kai Firamere 4 wanda zai anshi tamkar ka gama mai aiki zai karanta su".
Ita ma hukumar da ke kula da makarantu a yankin Mani ta yaba da wannan gudumawa, a ta bakin sakataren ilimin karamar hukumar. "Ba karamin taimako zai yi ba, domin a halin yanzu muna da gibi na malamai tin fil'azan an dade da wannan matsalar malaman mutane na aje aiki babu daukar malamai, to mu wajen mu ai ba karamin al'amari ba ne ba. Dadi muke ji kwarai da gaske kuma za su taimaka wa ilimin ya daukaka ya kai wata turba wadda ba'a ma tunani insha Allahu" .
Umar Babani Isa shi ne hakimin Mani, ya yi godiya a madadin iyaye "Wannan ba karamin abun alfahari ba ne kwarai da gske, kuma mun ji dadin yadda suka yi kuma ganin cewa dukkan su wadanda suka aje aikin nan malaman makaranta ne, wadanda suka fara tun daga Grade 2 har zuwa NCE da sauransu, saboda haka sun faro yadda ya kamata"