Kotun Saliyo ta nemi a maida shariar Charles Taylor zuwa Hague
March 31, 2006Charles Taylor,madugun yan tawaye daya zama shugaban kasar Liberia,ana ganin yana daya daga cikin manyan shugabannin da suke da hannu cikin yake yaken basasa a Liberia da makwabciya Saliyo,tsakanin 1989 da 2003,inda cikinsu akalla mutane 400,000 suka rasa rayukansu.
Kotun kasa da kasa dake sauraron laifukan yaki dake da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya a Saliyo dai,tana zargin Taylor,dan shekaru 58,da laifuka 11 yanzu,wadanda suka hada da take hakkin bil adama,kisan kiyashi da tilasata yara kanana shiga aiyukan soji.
Saboda ganin cewa,har yanzu Taylor yana da goyon baya daga wasu jamaar yankin,kotun ta Saliyo ta fadawa mahukuntan kasar Netherlands cewa,kasancewarsa a Saliyo zai jefa zaman lafiya na yankin cikin matsala.
A halin da ake ciki dai dakarun Majalisar dinkin Duniya sun karfafa matakan tsaro,a yankin da Charles Taylor yake tsare tare da wasu masu laifi su 9.
Jamian tsaro dauke da bindigogi suke gadin kofar,gidan yari da Taylor yake,tare kuma da wasu da suma suke dauke da bindigogi daka iya kare harin jiragen sama sanye da tabarau mai hangen nesa a saman ginin da Taylor yake.
A dai ranar laraba ne aka kama Charles Taylor kusa da bakin iyaka Najeriya da Kamaru,kwanaki 2 bayan tserewarsa daga inda yake zaune tun zuwansa gudun hijira Najeriya tun 2003.
Najeriyar dai ta fuskanci matsin lamba na kasashe,domin ta mika Charles Taylor,bayan shugabar Liberia Ellen Johnson Sir-Leaf ta bukaci,a mika shi domin ansa laifukan da ake zarginsa da su a gaban kotun dake Saliyo.
Babban mai daukaka kara Desmond Da Silva,ya fadawa manema labarai jim kadan bayan rufe Taylor a daya daga cikin dakunan kurkuku 18 na kotun cewa,nan bada jimawa bane Charles Taylor zai baiyana gaban kotu,amma ainihin shariar tasa zai dauki watanni.
An zargi charles Taylor da daukar nauyin wata kungiyar yan tawaye ta marasa imani wato RUF,wadda ta yanyanka mutane,fyade da bautar da dubun dubatar farar hula a lokacin yakin basasa na Saliyo,daya daga cikin yake yaken basasa mafiya muni a tarihi.
A can babban birnin kasar Liberia,uwargidan Charles Taylor,JewelHoward Taylor,ta bukaci yan uwa da abokan arzikin tsohon shugaban da su kwantar da hankulansu,a wannan lokaci wadda ta kira nab akin ciki daya same su.
Tun farko shugaba Johnson Sirleaf tayi gargadin shiga kafar wando daya da,duk wani dan kasar ta Liberia da yayi kokarin yin anfani da batun tsare Taylor da akayi ya bullo da tashe tashen hankula a kasar.