1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ICC za ta gudanar da bincike kan mummunan rikicin Burundi

Mohammad Nasiru AwalApril 25, 2016

Akalla mutane 430 aka kashe sannan dubbai sun tsere zuwa ketare tun bayan barkewar rikicin siyasar Burundi a watan Afrilun 2015.

https://p.dw.com/p/1IcTu
Niederlande Den Haag Gerichtsvollzieherin Fatou Bensouda beim Fall Jean-Pierre Bemba
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Lampen

Mai gabatar da kara a kotun kasa da kasa Fatou Bensouda ta ce za ta bude wani bincike na wucin gadi dangane da mummunan tashin hankalin da ya barke bara a kasar Burundi da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane sannan ya tilasta dubun dubata tserewa zuwa kasashen ketare. Ofishin hukumar kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kiyasin cewa akalla mutane 430 aka kashe tun bayan barkewar rikicin a watan Afrilun 2015, lokacin da Shugaba Pierre Nkurunziza ya kaddamar da aniyar neman wa'adin mulkin karo na uku, sannan ya lashe zaben da aka gudanar a watan Yulin da ya biyo baya. A lokacin da take bayyana matakin fara gudanar da bincike Bensouda ta ce.

"Ofishi na ya duba bayanai da rahotanni game da kashe-kashe da daure mutane a kurkuku da cin zarafi da fyade da sauran ta'asa ta bacewar mutane. Kasancewa wadannan batutuwa na karkashin hurumin kotun ICC, na yanke shawarar bude binciken wucin gadi kan halin da Burundi ta samu kanta ciki tun a watan Afrilun 2015."