Kotun laifuka ta birnin Heague ta ki yarda da bukatar Gbagbo
October 27, 2015Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC a ranar Litinin ta yi watsi da bukatar lauya da ke kare tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo ta neman a maida sauraran karar wanda yake karewa zuwa birnin Abidjan, abin da kotun ta ki amincewa bisa dalilan da kotun ta danganta da matsalar tsaro.
Wannan mataki da kotun da ke a birnin Hague ta dauka dai na zuwa ne bayan da a watan da ya gabata lauyan tsohon shugaba Gbagbo ya nemi a mayar da sauraren karar zuwa Kudancin kasar ko kuma a kai ta zuwa birnin Arusha na Tanzaniya.
A ranar 10 ga watan Nuwamba ne dai shugaba Gbagbo tare da jagoran 'yan tawaye da ke tare da shugaba Gbagbo Charles Ble Goude za su bayyana a gaban kotun saboda hannunsu a rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa a shekarar 2010 abin da ya yi sanadin rasa rayukan mutane 3000.