1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ICC ta yanke wa Bemba hukunci

September 17, 2018

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta tabbatar da daurin shekara guda kan madugun 'yan tawayen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/352cF
DR Kongo Jean-Pierre Bemba
Hoto: Getty Images/AFP/P. Mulongo

Kotun da ke hukunta manyan laifuka ta duniya ta ICC ta tabbatar da hukuncin daurin shekara guda da wata kotu ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, Jean-Pierre Bemba.

Shi dai Mr. Bemba an zarge shi ne da kokarin bai wa shaidu cin hanci a babbar shari'arsa kan laifukan yaki a shekara ta 2016.

Yanzu dai Kotun ta ICC ta ce Jean-Pierre Bemban ba zai yi wani zama a gidan yarin ba, saboda idan aka fidda adadin zaman da ya yi a baya, to ya kammala adadin zaman da aka yanke masa kenan.

Tuni  dai aka mayar da martani kan wannan hukunci da ma matsayin tsohon madugun 'yan tawayen na Kwango, wanda ya nemi tsayawa takarar shugabancin kasa, ko da yake bai yi nasara ba.

Yanzu dai bakin alkalami ya bushe wa Mr. Bemba dangane da takarar shugabancin kasar.