Kotun ICC ta yanke hukumci akan Thomas Lubanga
July 10, 2012Kotun duniya ta ICC da ke hukumta man'yan laifufuka ta yanke wa tsohon jagoran ƙungiyar mayaƙan sa kai na Kwango Thomas Tubanga hukumcin daurin shekaru 14 na zama gidan jarum.Lubanga dan shekaru 51 da haifuwa wanda ake tsare da shi tun a shekara ta 2006, kotun ta same shi da aikata laifufukan yaƙi na yin amfanin da ƙanana yara yan ƙasa da shekaru 15 a matsayin soji, tare da aikta kisan gila akan fararan hula:
A yaƙin basasar da aka gwabaza a yaƙin Ituri da ke a sahen arewa maso gabashin jamhuriyar Dimokaradiyar kwango a sheku 2002 zuwa 2003.Tsohon mataimakin jagoran ƙungiyar mayakan na FPLC dake sanye da kot. toka toka da fara riga daga ciki, wada ya musuntu laifufukan da ake tuhumar sa da aikatawaya yi tagumi a lokacin da alƙalin kotun adrian fulford ya baiyana hukumci a birnin hake wanda ya ce za a fara lisafin ne tun lokaci da aka tsare shi.Wannan dai shine hukumci na farko da kotun ta yanke tun a shekara ta 2003 da aka girkata.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu