Jean-Pierre Bemba ya kubuta daga kotun ICC
June 8, 2018A shari'ar farko dai kotun mataki na farko ta ICC ya yanke masa hukunci dauri na tsawon shekaru 18 a gidan kaso kan zargin aikata manyan laifukan da mayakansa suka tafkan a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Sai dai kuma sashen daukaka kara na kotun ta ICC ya soke shari'ar farko sannan kuma ya wanke shi daga zargin da ake yi masa, a cewar alkalin kotun daukaka karan Christine van den Wyngaert, babban kuskuren da kotun ta farko ta tafka, shi ne ya shafe dukkan laifukan da ake zargin Bemba da aikatawa.
Tsohon hamshakin dan kasuwan na kasar Kwango da ya rikide ya koma madugun 'yan tawaye, an tuhume shi ne kan irin ta'asar da mayakansa na kungiyar MLC suka tafka a tsakanin shekara ta 2002 zuwa 2003, inda a shekara ta 2006 aka kama shi da laifin kashe-kashen jama'a da cin zarafin mata da mayakansa suka yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.