Kotun ICC ta tuntubi Saif al-Islam Gadhafi
October 28, 2011Kotun hukunta miyagun laifuka ta kasa da kasa dak e a brinin the Hauge na kasar Holland wato ICC ta ce ta tuntubi Saif al-Islam dan marigayi Muammar gadhafi bisa yiwiuwar mika kansa gareta. Tun bayan da mayakan sabbbin shugabannin Libiya suka kashe mahaifinsa a wajen garin Sirte ne Saif ya arce zuwa jamhuriyar Nijar inda Luis Moreno Ocampo, jami'in shigar da kara a kotun ya ce sun samu damar tuntubarsu ta hanyar masu shiga tsakani . Ofishin jami'in ya ce in har ya mika kansu ga kotun za a saurare shi kuma ba za a dora masa laifi har sai an samu shedar da ke tabbatar da haka. Jami'in ya kara da cewa wasu kafafe da ba a tantace ba sun ba da abarin da ke nuni da cewa akwai gungun sojojin haya da suka yi tayin fita da Saif zuwa wata kasa ta Afirka da ba ta rattaba hannu kan dokar Rome da ta kafa kotun ta ICC ba.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Zainab Mohammed Abubakar