Kotun ICC ta tabbatar da shari'ar Lubanga
December 1, 2014A yau Litinin ne kotun hukunta masu aikata muyagun laifuka ICC da ke birnin Hague, ta tabbatar da daure madugun 'yan tawayen Kwagon nan wato Thomas Lubanga, lamarin da ya kawo karshen lokaci mai tsawo da aka kwashe ana shari'ar.
Tun cikin shekara ta 2006 ne dai aka soma wannan shari'ar, shekaru biyu da suka gabata kuma aka yanke masa hukuncin dauri na tsawoin shekaru 14, musamman saboda amfani da yayi da kananan yara a matsayin soji a rikicin Kwangon da aka yi a tsakanin shekarun 2002 zuwa 2003.
Lubanga ya daukaka kara ne bayan da ya gabatar da wani faifain bidiyon da ke nuna cewa sojojin da ya yi amfani da su ba kananan yara bane.
Sai dai, alkalin da ya yanke masa hukuncin a yau Erki Kurula, ya ce bai ma ga wani dalilin yin wata tababa kan hukuncin farko da aka yankewa madugun tawayen na Kwangon Thomas Lubanga ba, saboda a cewar sa an bi duk wasu hanyoyin da suka dace a hukuncin.