Kotun ICC na sauraron ƙara a kan kisan kiasun Ruwanda
October 22, 2012Kotun duniya da ke hukumta man'yan laifuka na yaƙi ta fara sauraron ƙarar wata mata yar Hollande,yar asilin ƙasar Ruwanda Yvonne Basebya, akan tuhuhumar da ake yi ma'ta da hannu a kisan kiasun da aka aikata akan miliyoyin jama'a a shekara ta 1994 a Ruwanda galibi yan ƙabilar tutsi.
A lokacin da aka buɗe zaman kotun babban alƙali mai gabatar da ƙara Ward Fernandusse, ya ce uwargida Basebya yar shekaru 65 da haifuwa na da hannu wajan yin feyɗe da kisan yan ƙabilar tutsi akan manufar kisan ƙare dangi ga ƙabilar. akan rawar da ta taka wajan aikata kisa akan wasu yan tutsit 110 wanda suka samu mafuka a cikin wata cocin a birnin Kigali a farkon shekaru 1994.Kuma zata iya fuskantar hukumcin ɗaurin rai da rai inda har aka sameta da laifin .
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasir Awal