Kotun ICC na son bayanin Afirka ta Kudu kan al-Bashir
September 7, 2015Kotun ICC da kan hukunta wadanda suka aikata manyan laifuka ta bukaci kasar Afirka ta Kudu ta yi bayani kan dalilan da ya sanya ta gaza kama shugaba Omar al-Bashir a watan Yuni lokacin da ya shiga kasarta duk kuwa da cewar mahukuntan kasar sun sani ya na da sammacen kasa da kasa da aka lika masa ne neman a mikashi ga kotun.
A wani umarni da kotun ta birnin Hague ta fitar a ranar Litinin din nan ta ce mahukuntan na birnin Pretoria na da dama daga nan zuwa ranar biyar ga watan Oktoba mai zuwa su bada bahasi kan dalilan rashin kamun na al-Bashir da ya halacci taron koli na kungiyar kasashen Afirka ta AU.
Kotun ta ICC dai na neman shugaba al-Bashir ruwa a jallo bisa zarginsa da laifukan yaki da take hakkin bil'Adama a rikicin yankin Dafur.